Dabarun Sojoji Na Yaki Da Ta’addanci Ba Ya Aiki – Gwamnan Kebbi

[ad_1]


Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya yi kira ga sojoji, su sauya dabarun da suke amfani da su wajen kokarin magance matsalar rashin tsaro.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi, a ranar Litinin da ta gabata.

Har ila yau, gwamnan ya kuma kara jaddada kiransa na a binciki batun janye jami’an soji da aka tura makarantar sakandiren ’yan mata ta gwamnati da ke Maga, ‘yan mintuna kadan kafin barayin su sace ‘yan mata su goma sha biyu.

“Ta yaya ‘yan bindiga sama da 500 za su rika tafiya a kan babura bisa manyan hanyoyinmu, ba tare da an tantance su ba, muna yin aikin da ya rataya a wuyanmu na jami’an tsaro, muna kuma ba su kayan aiki, sannan mun sayo musu motoci sama da guda 100, amma duk da haka; harkokin tsaro ba su inganta ba.

“Da a ce mun san za su bari wadannan barayi su yi awon gaba da ‘yan matanmu, da ba mu saurari shawarar da suka ba mu ta tura jami’an tsaro ba, da tuni mun rufe makarantun baki-daya.

“Ina ganin wasu makiya suna kokarin durkusar da wannan gwamnati da ta tarayya, sannan kuma dole ne majalisa ta yi wani abu, musamman a kan matsalar tsaro da kasar nan ke fama da shi.

“Jiya Kebbi ce, yau kuma Neja da Kwara, wa ya san wanda zai biyo baya kuma? Don haka, dole ne dukkaninmu mu tabbatar da ganin an magance wannan matsala ta rashin tsaro.”

Tun da farko, Kakakin Majalisar Tajudeen ya bayyana cewa; shi da wakilan majalisar, sun je Kebbi ne domin jajanta wa jama’arta game da sace ‘yan matan da aka yi da kuma kashe shugaban jami’an tsaro na cibiyar.

Shugaban majalisar ya kuma bayar da gudunmawar Naira miliyan 30 ga iyalan shugaban jami’an tsaro na makarantar da sauransu.

Ya ce, “Muna tare da ku, sannan kuma za mu ci gaba da nemo yadda za mu tsare wadannan ‘yan mata.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *