Fadin Filaye Masu Dausayi Na Sin Ya Kai Matsayi Na Hudu A Duniya

[ad_1]

Yau Litinin 2 ga wata ranar kiyaye filaye masu dausayi ta duniya ce. Hukumar kula da gandun daji da ciyayi ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tana ci gaba da yin kokarin kiyayewa da gyara filaye masu dausayi, sakamakon haka, fadin filaye masu dausayin kasar Sin ya kai matsayin koli a nahiyar Asiya, kuma ya kai matsayi na hudu a duniya, a sa’i daya kuma, an tsara sabon tsarin kiyaye filayen a kasar.

Filaye masu dausayi suna taka rawar gani a fannin kiyaye halittu, da zamantakewar al’umma, da tattalin arziki, da kuma al’adu. Cikin shekarun baya bayan nan, kasar Sin tana kara karfafa aikin kiyaye filaye masu dausayi bisa doka, kuma hukumomin da abin ya shafa sun kammala aikin kyautata dokokin kiyaye filayen na matsayin lardi a larduna da birane da yawansu ya kai 21 a fadin kasar ta Sin. (Mai fassara: Jamila)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *