An ƙone ‘ɓarawon’ babur ƙurmus a Binuwai

[ad_1]



Jama’ar gari sun kone wani mutum da ake zargi da satar babur da safiyar Talata a kan titin Ibrahim Kashim Road da ke Makurdi, babban birnin jihar.

Wani ganau da ya ce sunansa Andrewa Tergu, ya shaida wa wakilinmu cewa fasinjoji biyu ne suka hau kan babur din wani dan acaba da nufin ya kai su unguwar Railway Quarters a garin na Makurdi.

Sai dai dan acabar bai sani ba, ashe akwai wani mutum daya da yake tsaye a daidai inda zai sauke fasinjojin, inda yake tsaye yana jiran su isa.

Da isar su, sai ya sa hannun a aljihu kamar zai ciro kudi ya sallami dan acabar, amma sai ya zaro almakashi ya caccaka masa a wurare daban-daban.

Andrew ya ce dan acabar ya fado daga kan babur din nasa inda ya rika ihun neman taimakon mutanen gari.

“A kokarin barayin na guduwa ne daya daga cikinsu ya fado daga kan babur din da suka sata, inda mutane suka far masa da duka, suka jawo shi kan titi sannan suka banka masa wuta,” in ji Andrew.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, lokacin da wakilinmu ya ziyarci inda wurin ya faru, ya iske jami’an Hukumar Tsaftace Muhalli ta Jihar suna kokarin share wurin da aka kone wanda ake zargi da satar babur din.

Da muka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da faruwar lamarin sannan ta yi alkawarin ba wakilinmu cikakken bayani daga bisani.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba ta kai ga yin hakan ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *