’Yan bindiga sun sace sakataren ƙaramar hukuma a Kano
’Yan bindiga sun kai hari gidan sakataren Ƙaramar Hukumar Kibiya a Jihar Kano, tare da yin awon gaba da shi.
Shugaban kansiloli na ƙaramar hukumar, Hon. Sabo Yusuf Usman, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma’a a gidan sakataren da ke garin Dinya.
Ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 1 na dare, lokacin da sakataren ke barci a gidansa.
A cewarsa, maharan sun fara tayar da ɗan sakataren da ke kwance a harabar gida, sannan suka tilasta masa ya buga ƙofa ya yi kamar yana fama da ciwon ciki.
“Da yaron ya buga ƙofa, mahaifinsa ya tambaye shi ko wane ne. Yaron ya ce shi ne, ya ce yana fama da ciwon ciki ne.
“Da mahaifin ya buɗe koda, sai ’yan bindigar suka tafi da su gaba ɗaya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa daga baya maharan sun saki yaron, amma suka tafi da sakataren.
Jami’an tsaro sun isa wajen bayan faruwar lamarin, amma ba su samu kowa ba domin sun tafi.
Ƙaramar Hukumar Kibiya ba ta saba fuskantar irin waɗannan hare-hare ba.
Sai dai, maƙwabtan ƙananan hukumomi irin su kamar Tsanyawa da Shanono, waɗanda ke maƙwabtaka da Jihar Katsina, sun sha fama da hare-haren ’yan bindiga a baya.