Motoci da shaguna sun kone a gobarar Garejin Buzaye da ke Sakkwato




Gobara ta cinye motoci da shaguna a babbar kasuwar kayan motoci ta kasa da kasa da ke Sakkwato, wadda aka fi sani da Garejin Buzaye da ke Sakkwato.

Wakilinmu ya ruwaito cewa shaguna da motoci da sauran kadarori sun kone a gobarar da ta tashi da misalin karfe 10 na safiyar Litinin.

A lokacin da ake rubuta wannan rahoto, jami’an kashe gobara na ci gaba da ƙoƙarin shawo kan wutar.

Rahotanni sun ce ana zargin gobarar ta samo asali daga matsalar lantarki, inda wutar ta shafe sa’o’i tana barna, duk da ƙoƙarin da Hukumar Kasar ta kashe gobara, da mazauna yankin suka yi.

Wani mai gyaran mota da ke wurin ya bayyana cewa akalla shaguna 40 ne suka salwanta, tare da sassan da aka ware don gyaran motoci irin su Marsandi, da kuma shagunan sayar da kayan ajiya.

Wasu daga cikin motocin da gobarar ta shafa ma daga Jihar Sakkwato ne, wasu kuma daga ƙasar Jamhuriyar Nijar.

Shugaban ƙungiyar Kanikawa ta Najeriya (NATA), reshen Garejin Buzaye, Injiniya Abdulkadir Muhammad, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.

Ya ce, “Har yanzu ba za mu iya tantance adadin shaguna da motoci da aka lalata ba, domin gobarar na ci gaba da ci. Za mu iya sanin girman asarar ne bayan an kashe wutar gaba ɗaya.”

Ya danganta gobarar da matsalar lantarki, tare da nuna cewa kasancewar wurin na cike da kayan da ke iya kamawa da wuta da kuma abubuwan iskar gas da ake amfani da su wajen walda, ya ƙara ta’azzara lamarin.

Injiniya Muhammad ya roƙi gwamnatin Jihar Sakwkato ta kawo tallafi ga waɗanda abin ya shafa, saboda

Ya tuna cewa tallafin da aka samu daga gwamnati bayan irin wannan gobara shi ne a zamanin tsohon gwamna Aliyu Wamakko, fiye da shekaru goma da suka wuce.

Ya ce duk da irin roƙon da aka yi a baya, ba a samu tallafi ba daga gwamnatin da ta gabata.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *