Jarin Da Kamfanonin Sin Suka Zuba A Sassan Ketare Ya Samu Ci Gaba Bisa Daidaito A 2025

[ad_1]

Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayyar kasar Sin He Yongqian, ta ce jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a sassan ketare a shekarar 2025 da ta gabata, ya bunkasa bisa kyakkyawan yanayi, da daidaito da tsari, wani ci gaba da ya samu sakamakon aiwatar da hadin gwiwa mai matukar inganci, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.

He Yongqian, wadda ta bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum, ta ce ya zuwa karshen shekarar ta 2025, masu zuba jari na kasar Sin sun kafa kamfanoni sama da 50,000 a kasashe da yankunan duniya 190, kana jimillar jarin da suka shigar sassan ketare na cikin uku na kan gaba a duniya, cikin shekaru tara a jere.

Kazalika, darajar jarin da masu zuba jarin na kasar Sin suka shigar a sassan ketare ya kai dalar Amurka biliyan 174.38 a shekarar da ta gabata, karuwar da ta kai ta kaso 7.1 bisa dari, sama da na shekarar da ta gabaci hakan, kuma yana cikin mafiya yawa a duniya baki daya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *