Sojoji Sun Gano Ƙungiyar Safarar Makamai A Taraba
[ad_1]
Sojojin rundunar 6 Birget, Sashe na 3, ‘Operation Whirl Stroke’, sun sami nasara a yakin da ake yi da safarar makamai a jihar Taraba bayan wasu ayyukan leken asiri da suka kai ga kamawa da kuma kwato makamai.
A cewar wata sanarwa da Laftanar Umar Muhammad, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar ya fitar, ta ce, an gudanar da ayyukan ne tare da hadin gwiwar jami’an Hukumar Leken Asiri ta Tsaro.
- Yawan Hatsin Da Kasar Sin Ta Noma Ya Kai Wani Sabon Matsayi Na Koli A 2025
- Zamfara: PDP Ta Yaba Wa Kotun Abuja Kan Nasarar Da Ta Samu
Lit. Muhammad ya bayyana cewa, an fara kama mutane biyu da ake zargi da safarar bindigogi, wadanda aka bayyana su da Mr. Christopher Adamu da Mr. James Yangyang, a mahaɗar Sebos da ke Mayo Dassa, karamar hukumar Jalingo, da kuma Kauyen Tautre da ke karamar hukumar Ardo-Kola a ranar 11 da 12 ga Janairu, 2026.
Bisa ga waɗannan nasarorin, sojojin sun ƙaddamar da wani aikin sintiri da bincike a ƙauyen Murubai da ke ƙaramar hukumar Ardo-Kola, hakan ya yi sandin gano bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, mujalla ɗaya, da harsasai huɗu a gidan Mista Bazoe John, wanda ake zargi da safarar makamai wanda a halin yanzu ake nema ruwa a jello.
Ya ce, ana ci gaba da ƙoƙarin kama wanda ake zargin domin kamo sauran makaman da ya yi safararsu.
[ad_2]
Source link