Sin Ta Mika Sakon Ta’azziya Sakamakon Gobara Da Ta Kone Wani Babban Kanti A Pakistan

[ad_1]

Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda game da wata gobara da ta kone wani babban kantin sayar da kayayyaki dake kasar Pakistan, ya ce Sin ta samu labarin aukuwar wannan mummunan lamari. Ta kuma mika sakon ta’aziyyar wadanda suka rasu yayin gobarar, tare da fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata.

Dangane da kalaman kakakin NATO game da Greenland kuwa, Guo ya bayyana cewa, Sin ta dage kan kula da dangantaka tsakanin kasashen duniya, bisa manufofi da ka’idojin tsarin dokokin Majalisar Dinkin Duniya. Kuma batun nan na “barazanar Sin”, ba shi da tushe ko kadan, kana kasar Sin tana adawa da kirkirar wani batu marar tushe, da kuma amfani da kasar Sin a matsayin wata hujjar neman biyan bukatu na kashin kai.

Da ya tabo batu kan ziyarar aikin da firaministan Finland Petteri Orpo zai yi a Sin kuwa, Guo Jiakun ya ce Sin tana mayar da hankali matuka ga ci gaban dangantakar Sin da Finland, kuma tana fatan ci gaba da musayar ra’ayi mai zurfi tsakanin manyan jami’ai da kasar ta Finland, domin daga dangantakar bangarorin biyu zuwa wani sabon mataki tare. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *