Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
A yau Lahadi, sojojin kasar Sin sun bukaci kasar Philippines da ta gaggauta dakatar da tayar da zaune tsaye da kara ruruta wutar rikici a tekun kudancin kasar ta Sin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin (PLA), Tian Junli, ya bayyana hakan, biyo bayan wani aikin sintiri na hadin gwiwa da kasar Philippines ta yi da kasashen da ba su da alaka da yankin, lamarin da ya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Mai magana da yawun rundunar ya kuma bayyana cewa, a ranar Jumma’ar da ta gabata, rundunar ta PLA mai kula da yankin kudancin Sin ta shirya wata tawagar jiragen saman yaki domin gudanar da sintiri na yau da kullum a tekun kudancin Sin.
Kazalika, a yau Lahadi, rundunar tsaron gabar tekun kasar Sin (CCG) ta yi sintiri a yankin ruwan Diaoyu Dao na kasar.
Sanarwar da CCG ta fitar ta ce, an gudanar da sintirin ne domin kare hakkin kasar Sin a karkashin doka. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)