Tottenham ta sallami kocinta Thomas Frank

[ad_1]



Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur ta sallami kocinta, Thomas Frank bayan watanni takwas kacal da karɓar ragamar horas da ’yan wasanta.

Tottenham ta kori Frank ne bayan shan kashi 2-1 a gida a hannun Newcastle ranar Talata, lamarin da ya bar Spurs da tazarar maki biyar kacal tsakaninta da rukunin faɗawa zuwa ajin Championship.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa sallamar kociyan na da nasaba ne da rashin kataɓus, inda a bayan nan ƙungiyar ba ta samu nasara ba a wasanni takwas da suka gabata a Premier League.

Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana Frank a matsayin “ƙwararren koci kuma mutum na musamman”, amma ya ce a harkar ƙwallo kowa na fuskantar barazanar kora saboda sakamako ne ke yanke hukunci.

Frank mai shekara 52 shi ne koci na bakwai da aka kora a Premier League a kakar bana.

A halin yanzu, Arsenal da ke jan ragamar teburin babbar gasar ta Ingila za ta ziyarci Tottenham a wasan hamayya na arewacin Landan a mako mai zuwa.

A gefe guda, tsohon kocin Spurs, Harry Redknapp mai shekara 78 ya ce zai ji daɗin komawa idan aka nemi ya riƙe muƙamin riƙon ƙwarya, sai da ya bayyana cewa da wuya hakan ta faru.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *