Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Gombe, ta fara aikin gyara da sake duba hanyoyin kiwo 37 tare da filayen kiwo takwas a faɗin jihar.

Wannan aiki na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage rikici da ake samu tsakanin manoma da makiyaya.

An gudanar da aikin ne ƙarƙashin shirin ‘Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES)’ a matsayin wani ɓangare na gwamnatin jihar don samar da zaman lafiya.

Shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana cewa ana fuskantar matsaloli ne saboda lalacewar hanyoyin kiwo da gonaki.

A baya-bayan nan, tawagar shirin tare da jami’an tsaro, shugabannin gargajiya da jagororin makiyaya, sun kai ziyara ƙauyen Kunji da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba don sauraron ƙorafe-ƙorafen jama’a.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa za a ci gaba da tattaunawa da dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa domin samar da mafita mai ɗorewa da kuma hana aukuwar rikici.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *