Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki

[ad_1]



Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu.

Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rabon gidaje 72 ga malamai da ma’aikatan lafiya a ƙaramar hukumar Mafa.

Zulum ya ce Marbel ta shafe fiye da shekaru 24 tana aiki a cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke Mafa, kuma ba ta taɓa barin wurin ba ko da a lokacin rikicin Boko Haram.

“Ko da rikici ya yi tsanani, ba ta taɓa barin Mafa ba, duk da cewa ba ’yar asalin jihar ba ce. Ta kula da ’yan uwana da dama, har da mahaifiyata. Wannan ya sa ta cancanci a girmama ta,” in ji Zulum.

Gwamnan ya bayar da umarnin a bai wa ma’akaciyar gidan da sunanta, tare da sanar da cewa ɗanta, Anthony Duaka, wanda ya kammala karatun banki, an bas hi aiki kai tsaye a Jami’ar Kashim Ibrahim da ke Maiduguri.

A cikin martaninta, Marbel ta bayyana farin cikinta da godiya ga gwamnan bisa karramawar da ya yi mata.

“Yau ce rana mafi farin ciki a rayuwata. Gwamna ya karrama ni fiye da tsammanina. Ya ɗauki nauyin karatuna na digiri a fannin lafiya, ya ba ɗana aiki, yanzu kuma gida. Na gode ƙwarai,” in ji ta.

Wannan mataki ya biyo bayan irin na shekarar 2022, lokacin da Gwamna Zulum ya bai wa wata malamar makaranta ’yar ƙabilar Igbo, Misi Obiageli Mazi, kyautar gida saboda jajircewarta da bin lokaci wajen zuwa aiki a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *