’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai
[ad_1]
Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya.
Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su.
Galibi dai ’yan ci-ranin da suka fito daga ƙasashen Afirka na ƙoƙarin tsallakawa nahiyar Turai ne domin samun ingantacciyar rayuwa.
Ko a ranar Laraba dai ma’aikatan ceto sun ce sun ceto mutum 60 da ransu, wadanda suka hada da maza 56 da kuma mata hudu, sannan aka kai su tsibirin na Lampedusa, kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a kasar ta Italiya ta tabbatar.
Kakakin Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM), Flavio Di Giacomo, ya ce akwai mutum 95 a cikin jiragen guda biyu da suka nitse.
Ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa, “kasancewar an ceto mutum 60 da rai, ana fargabar akwai mutum 35 da suka mutu ko kuma suka ɓace.“
Hatsarin wanda ya ritsa da ’yan ci-ranin da suka taso daga ƙasar Libya shi ne na baya-bayan nan ga mutanen da ke kokarin tsallaka teku domin shiga nahiyar Turai.
Alkaluma sun nuna daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, akalla mutum 675 ne suka rasa ransu ta irin wannan hanyar a kan iyakokin kasashen biyu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link