’Yan bindiga sun kashe tsohon malamin makaranta a Edo
[ad_1]
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani tsohon malami kuma manomi, Andrew Imuekheme, a Jihar Edo.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata a garin Ikabigbo, da ke Masarautar Uzairue, a Ƙaramar Hukumar Etsako ta Yamma.
Rahotanni sun ce Malam Andrew na kan hanyarsa daga gona lokacin da maharan suka tare shi, tare da ɗauke shi zuwa daji.
Wata mata da ta tsere daga hannun maharan ta koma cikin gari tare da sanar wa mafarauta, waɗanda suka fara bincike nan take.
Tuni jami’an tsaro suka umarci manoma da ke da gonaki a kusa da yankin da su koma gidajensu saboda tsaro.
Daga baya, ’yan sa-kai sun gano babur da takalman mamacin.
Bayan zurfafa bincike cikin dare suka gano gawarsa.
Sarkin garin, Cif Braimah Alegeh, ya yi Allah-wadai da kisan tare da bayyana mutanensa a matsayin masu zaman lafiya.
Ya roƙi gwamnati da jami’an tsaro su kawo musu ɗauki.
Wannan shi ne karo na uku da irin wannan kisan ke faruwa a garin.
Shekaru biyu da suka gabata, an kashe wani malamin Katolika da shugaban mafarauta.
Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Moses Yamu, ya ce zai fitar da sanarwa daga baya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link