Shawarar GGI Ta Sin Na Ingiza Daidaito Ga Duniya Mai Fama Da Tangal-Tangal

[ad_1]

Mahalarta taron karawa juna sani na kasa da kasa, na dandalin Baku karo na 13, sun bayyana gamsuwa game da tasirin shawarar inganta jagorancin duniya ko GGI, wadda kasar Sin ta gabatar, suna masu bayyana shawarar a matsayin wadda ke samar da daidaito ga yanayin duniya mai cike da sauye-sauye da tangal-tangal.

Da yake tsokaci game da hakan a taron na jiya Juma’a, tsohon wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin game da harkokin Turai Wu Hongbo, ya ce shawarar GGI, na yayata manufar martaba ikon kasashe na mulkin kai bisa daidaito, da nacewa biyayya ga dokokin kasa da kasa, da ingiza cudanyar mabanbantan sassa, da sanya bukatun bil’adama gaban komai, da manufar daura aniyar aiwatar da matakai a zahiri.

Wu ya kara da cewa, yayin da ake ganin karuwar manufofin daukar matsayar kashin kai da kariyar cinikayya, kana ake ganin fadadar rikice-rikice tsakanin mabanbantan yankunan duniya, da karin koma baya a tsarin jagorancin duniya, shawarar GGI ba kawai tana karfafa dalilai da ka’idojin kafuwar MDD ba ne, har ma ta zamo amsa ga burikan al’ummun kasa da kasa.

A nasa tsokacin kuwa, ministan raya tattalin arziki na kasar Azerbaijan Mikayil Jabbarov, bayyana goyon bayan kasarsa ya yi ga shawarar ta GGI. Yana mai cewa, tsarin gudanar duniya na yanzu na fuskantar tarin kalubale masu haifar da sauyi, amma duk da haka, kasar Sin ta samar da hanyar warware hakan, don wanzar da daidaito tsakanin sassan kasa da kasa.

Shi kuwa tsohon shugaban kasar Slovenia Borut Pahor, cewa ya yi kasar Sin ba ta shiga duk wasu nau’ikan tashe-tashen hankula, kuma ta nunawa duniya matakanta na koli, a fannin wanzar da daidaito, da tsayawa kan yanayi na tabbas, wanda hakan ya sanya ta zama muhimmin ginshiki na samar da daidaito a duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *