Mutum 6 sun rasu, 9 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
[ad_1]
Aƙalla mutum shida ne suka riga mu gidan gaskiya, yayin da wasu tara suka ji jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Jihar Kogi.
Hatsarin ya auku ne a daren ranar Alhamis a kan hanyar Lokoja zuwa Obajana, inda wata motar haya ƙirar Toyota Hiace ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota.
Shaidu sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne a yankin Apata, lokacin da motar hayar mai lamba XW 142 ENU ta yi karo gaba-da-gaba da wata tirela mai lamba KAB 575 XA wadda ta taho daga ɗaya hannun.
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar hatsarin a ranar Asabar.
Kwamandan hukumar na shiyyar Jihar Kogi, Tenimu Yusuf Etuku, ya bayyana hatsarin a matsayin abun tausayi, yana mai cewa gudun wuce ƙima ne ya haddasa shi.
Ya bayyana cewa jimillar mutane 17 ne hatsarin ya rutsa da su; maza 14 da mata uku.
A cewarsa, mutane tara (maza takwas da mace ɗaya) sun jikkata, yayin da mutum shida (maza biyar da mace ɗaya) suka rasa rayukansu.
Sauran mutum biyu kuma an ceto su ba tare da sun ji rauni ba.
Etuku, ya ƙara da cewa an kai waɗanda suka jikkata Asibitin Fisayo da ke Obajana domin kula da su, yayin da aka kai gawarwakin waɗanda suka rasu ɗakin ajiye gawarwaki na Ankuri da ke Lokoja.
Kayayyakin da aka samu bayan aukuwar hatsarin sun haɗa da kuɗi Naira 20,800, jakunkuna biyu, wayoyin hannu guda biyu, da wasu buhunhuna guda uku.
An kuma miƙa motocin da suka yi hatsarin ga rundunar ’yan sanda da ke Obajana.
Daga ƙarshe, kwamandan ya shawarci direbobi da su guji gudun wuce ƙima a manyan hanyoyi domin rage aukuwar hatsari da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link