Gwamnatin Tarayya Ta Biya ‘Yan Wasan Super Eagles Haƙƙoƙinsu
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da bayar da kyaututtukan wasanni ga ‘yan wasan Super Eagles da ke buga gasar cin kofin ƙasashen Afirka ta 2025 da ake gudanarwa a Morocco.
Bayan boren da ‘yan wasan suka yi a kan rashin biyansu haƙƙoƙinsu, ƙaramar ministar kuɗi, Misis Doris Uzoka-Anite, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a safiyar yau Alhamis.
- Majalisar Dokokin Ribas Ta Sake Fara Yunƙurin Tsige Fubara
- Shirin Ceto Zamfara Na Samun Nasara, Yayin Da Gwamna Lawal Ke Duba Ayyuka A Shinkafi
Uzoka-Anite ta ce gwamnati, tare da haɗin gwiwar Babban Bankin Nijeriya (CBN), ta warware matsalolin da suka dabaibaye tsarin biyan kuɗin ‘yan wasan domin tabbatar da biyan ‘yan wasa a kan lokaci.
“Ina farin cikin bayyana ci gaban da aka samu game da kyaututtukan wasanni ga tawagarmu ta ƙasa da ke buga gasar AFCON 2025,” in ji ta.
Ta ci gaba da cewa “Gwamnatin Tarayya tare da Babban Bankin Nijeriya sun yi nasarar daidaita tsarin musayar kuɗi na ƙasashen waje don tabbatar da cewa an ba ‘yan wasanmu kuɗaɗensu na lada ba tare da ɓata lokaci ba.”
A cewarta, an biya dukkan kyaututtukan ladan wasanni tun daga matakin rukuni har zuwa zagayen 16 gaba ɗaya.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa tawagar Super Eagles ta ƙaurace wa filin atisaye a wani yunƙurin nuna rashin jin daɗi dangane da tsaikon da aka samu wajen biyansu kuɗaɗensu na ladan wasanni, tare da barazanar ƙin zuwa Marrakech wajen buga wasanta na gaba da ƙasar Algeria da aka tsara gudanarwa matuƙar hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ba ta biya duka kyaututtukan ladan wasannin da suke bin ta ba.
[ad_2]
Source link