AFCON: Gwamnati za ta biya tawagar Super Eagles kuɗaɗen ihsani

[ad_1]



Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tawagar ’yan wasan Najeriya na Super Eagles na za su fara ganin kuɗaɗensu na ihsani na gasar cin kofin Afirka (AFCON) kafin ranar Juma’a.

A cewar karamar ministar kuɗi, Hon. Doris Nkiruka Uzoka-Anite, ’yan wasan za su karɓi kuɗaɗen ne wadanda suka tara tun lokacin zagayen rukuni.

Rahotonni sun nuna ’yan wasan sun tayar da tarzoma a sansanin Super Eagles ranar Laraba, saboda rashin biyan kuɗaɗen, inda ’yan wasan suka yi barazanar kin yin atisaye da kuma kin tafiya don fafatawar wasan dab da na kusa da na ƙarshe da za su fafata da Aljeriya a birnin Marrakesh.

NFF ta bayyana cewa za a fara aiwatar da biyan kuɗin, kuma Uzoka-Anite ta tabbatar da hakan, inda ta ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya, ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN), ta amince da bukatar ’yan wasan ya biyan su a kuɗaɗen ƙasashen.

Ta ce, “Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) sun yi nasarar sauƙaƙa tsarin musayar kuɗi don tabbatar da cewa ’yan wasanmu sun karɓi hakkokinsu ba tare da wani jinkiri ba.

“Daga yanzu, tsarin zai kasance mai sauƙi gaba ɗaya don tabbatar da biyan kuɗaɗe cikin sauri kuma bisa ka’idojin duniya.

“An saki dukkan kuɗaɗen ihsanin na zagayen rukuni gaba ɗaya kuma sun wuce matakan da ake buƙata.

“Ana kuma ƙoƙarin canza kuɗin zuwa na ƙasashen waje. ’Yan wasa za su iya ganin kuɗaɗen daga yau (Alhamis) ko gobe (Juma’a),” in ji ta.

Ta kuma tabbatar da goyon bayan Gwamnatin Tarayya kan jin daɗin ƙungiyar, domin Super Eagles su doke Aljeriya a ranar Asabar da kuma tabbatar da cewa sun kashe kofin AFCON daga ƙasar Maroko a karo na huɗu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *