Bidiyon Turji ya yamutsa hazo tsakanin Matawalle da Gwamnatin Zamfara
[ad_1]
Martani da muhawara sun ci gaba da biyo bayan matakin kotu da Ƙaramin Ministan Tsaron Bello Matawalle ya ɗauka kan waɗanda ke ƙoƙarin danganta shi da ayyukan shugabannin ’yan bindiga.
Jagoran ’yan bindiga, Bello Turji, ya saki bidiyo a shafukan sada zumunta inda ya goyi bayan tsarin sulhu da aka fara a lokacin gwamnatin Matawalle a Jihar Zamfara.
A cikin bidiyon, Turji ya soki abokin adawar sa, Musa Kamarawa, inda ya bayyana zargin da ya yi wa Matawalle a matsayin ƙarya mara tushe.
“Musa Kamarawa, duk zargin da ka yi ba gaskiya ba ne kuma ba su da tushe,” in ji Turji.
Ya ƙara da zargin cewa dangin Musa Kamarawa ne ke ƙara ta’azzarar matsalar ’yan bindiga ta hanyar nuna wariya ga Fulani makiyaya a yankunan Isa da Bafarawa na Jihar Sakkwato.
A wani bidiyo daban da tsohon Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Zamfara, Abubakar Dauran ya saki, ya zargi Gwamnatin Zamfara ta yanzu da ba wa Musa Kamarawa mafaka domin ɓata sunan Matawalle.
Dauran ya bayyana cewa an naɗa Musa Kamarawa a matsayin Mai Bayar da Shawara na Musamman (SSA) domin sauƙaƙa aiwatar da tsarin afuwa, sulhu da ajiye makamai.
“A matsayina na tsohon Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida kuma Shugaban Kwamitin Afuwa, Sulhu da Ajiye Makamai, mun yi aiki tare da Musa Kamarawa domin sauƙaƙa tsarin, wanda ya haɗa da jami’an tsaro da shugabannin al’umma,” in ji Dauran.
Ya ƙara da cewa lokacin da Matawalle ya hau mulki, ba shi da wani zaɓi illa ya rungumi tsarin sulhu saboda Zamfara tana cikin tashin hankali a lokacin.
A cewarsa, tsarin ya samu nasarori da dama, ciki har da ƙwato makamai masu haɗari da ceto dubban mutanen da aka yi garkuwa da su.
Dauran ya kuma zargi Musa Kamarawa da cin amana.
“Mun yarda da Musa Kamarawa, amma daga baya muka samu rahoton tsaro cewa ya sayi motar yaƙi. Wannan ne ya jawo aka kama shi a lokacin jagorancin Matawalle. Amma ba mu san yadda aka ba shi beli daga gidan yarin Kuje ba,” in ji Dauran.
Ya kuma yi alƙawarin ƙara fallasa wasu abubuwa a cikin bidiyo da zai sako nan gaba.
A cikin wata sanarwa, Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara, Dakta Jibo Magayaki, ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga Dauran, inda ya zarge shi da ƙoƙarin alaƙanta Gwamna Dauda Lawal da wannan rikici. Sanarwar ta fito ne daga Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Malan Halliru Andi.
A wata sanarwa ta daban, jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara ta zargi Gwamna Dauda Lawal da amfani da kuɗaɗen jihar wajen tallafa wa Musa Kamarawa da wasu domin ɓata sunan Minista Matawalle.
Sakataren Yaɗa Labarai na APC, Malam Yusuf Idris Gusau, ya bayyana cewa shugabancin jam’iyyar na jihar yana tsaye kan dukkan zargin da tsohon Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida, Abubakar Dauran, ya yi.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link