’Yan bindiga sun kashe mutane sun sace masu ibada a coci a Kogi

[ad_1]



Aƙalla mutane huɗu ne suka mutu yayin da ’yan bindiga suka sace mutane da ba a tantance adadinsu ba a wani coci da wasu wurare a Jihar Kogi.

’Yan bindiga sun kashe mutum guda tare da sace wasu da ba a tabbatar da iya yawansu ba a yayin da ake tsaka da ibada coci a ranar Lahadi a Jihar Kogi.

A safiyar ranar Lahadi ne maharan suka far wa masu ibadar a Cocin ECEWA da ke yankin Àaaaz-Kiri da ke Ƙaramar Hukumar Kabba/Bunu, bayan ’yan ta’adsan sun shiga yankin suna harbe-harbe, kai tsaye suka nufi cocin, a lokacin ana tsaka da ibada.

Wani mazaunin ƙauyen Àaaaz-Kiri da ke kusa da inda aka kai harin ya shaida wa wakilinmu da daddare cewa “Ba za a iya cewa ga haƙiƙnin yawan mutanen da aka kashe ba, amma ana tsaka da ibada da safe suka kawo harin.

“Zuwa yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, iyalai da dama kuma sun ba da rahoton rashin ganin ’yan uwansu bayan da’yan bindigar suka tafe ida mutane.

An kai hare-hare a lokaci guda

A wani lamarin kuma ’yan bindiga sun kashe mutane uku a wani hari da ɓata-gari suka kai har a ƙauyukan Illa da Okeagi da ke Ƙaramar Hukumar Mopa Muro.

Rahotanni sun ce maharan sun kai farmakin ne a lokaci guda, inda suka shafe fiye da awa guda sun cin karensu babu babbaka, kafin a iya isar da saƙon neman ɗauki ga jami’an tsaro.

Mazauna sun ce da farko sai da ’yan bindigar suka kai hari a yankin Jamroro inda suna kashe mutum biyu tare da jikkata wasu uku.

Wasu maharan kuma sun kashe mutum guda tare da sace wasu uku a wani harin da suka kai a wani yanki da ke maƙwabta da makarantar Ilai Grammar school.

Rahotanni sun bayyana cewa manoma ne akasarin mazauna yankunan Jamroro da kewayen yankin Ilai.

Sanata Sunday Karimi ya yi Allah wadai da yawaitar hare-haren, yana mai neman ɗaukin gaggawa daga jami’an tsaro.

Sanarwar da ya fitar ta ce, “Baya ga rahoton kisa da sace mutane da ba a tantance yawansu ba a Cocin ECWA da ke Àaaaz-Kiri a Ƙaramar Hukumar in Kabba/Bunu ranar Lahadi 14 ga Disamba, 2025.

“An kai makamancin harin a Oke-Agi da Ilai da ke Karamar Hukumar Mopamuro inda aka sace kashe mutum guda tare da sace wasu a al’umnar ƙabilar Tuve.”

Sanatan ya bayyana cewa hare-haren na ranar Lahadi sun tilasta wa mutane da dama a yankunan tserewa daga gidajensu, din haka ya yi kiransa a ɗauki tsauraran matakai don murƙushe ayyukan ’yan bindiga.

Ya kuma bayyana damuwa cewa sabon harin cocin ya faru ne ba da daɗewa ba bayan ’yan bindiga sun sace wasu masu ibada a Cocin Cherubim and Seraphim da ke Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas a Jihar.

Shi ma da yake jajen waɗanda abin ya shafa, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa ana ɗaukar matakan ganin an samu tsawon a kwanciyar hankali a yankunan Illai da Okeagi over the attack.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Mopamuro, Ademola Bello da a sarakunan gargajiya a yankunan sun tabbatar da hare-haren, Oke-agi and Ilai, inda rahotanni ke cewa sun je asibiti domin dubiyar mutane da a suka samu raunuka a hare-haren.

Zuwa lokacin da muka samu wannan rahoto dai kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kogi, CSP William Aya, bai amsa kira da sakonnin neman bahasi da wakilinmu ya tura masa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *