Dangote ya ƙulla yarjejeniyar gina kamfanin takin zamani na dala biliyan 2.5 a Habasha
[ad_1]
Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani ta kimanin dala biliyan 2.5.
Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis.
Abiy ya ce wannan yarjejeniya da Dangote Group na attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, za ta sanya ƙasarsa cikin jerin manyan ƙasashen da ke samar da takin zamani a duniya.



Ya bayyana cewa wannan aikin gina masana’antar wanda za a fara nan ba da jimawa ba, za ta riƙa samar da tan miliyan uku na takin zamani a kowace shekara.
“Wannan aikin zai samar da ayyukan yi ga ’yan ƙasa, ya tabbatar da wadatar takin zamani ga manomanmu da suka daɗe suna fama da ƙalubale.
“Sannan zai zama mataki na musamman a yunƙurinmu na cin gashin kai wajen samar da abinci,” in ji Abiy.
A watan Yuni, Aliko Dangote ya shaida cewa nahiyar Afirka za ta iya zama mai isar wa kanta da takin zamani cikin shekaru 40 bisa tsarin faɗaɗa masana’antarsa ta dala biliyan 2.5 da ke Legas.
A halin yanzu dai, Afirka na shigo da fiye da tan miliyan shida na takin zamani a kowace shekara, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link