An kama ’yan bindiga da makamai da miyagun ƙwayoyi a Kwara

[ad_1]



Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Kwara, ta ce ta kama wasu mutum biyu da ake zargi ’yan bindiga ne a wani samame da ta kai a unguwar Saminaka da ke Ƙaramar Hukumar Patigi.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Abubakar Jubril mai shekaru 28 da Mohammed Abubakar mai shekaru 26.

An kama su a ranar Talata, 3 ga watan Maris, 2026, bayan jami’an hukumar sun kai samame yankin.

A cewar hukumar, mutanen biyu na cikin wasu mutane da aka taɓa gani a wani yanki da ke fama da tashin hankali.

An samu nasarar kama biyu daga cikinsu, yayin da ɗaya ya tsere kuma har yanzu ana nemansa.

Kayan da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da bindiga ƙarama mai lamba 7886 wadda aka ƙera a Amurka, wayar hannu, ƙwayoyin tiramol da kuma sigari.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai a Ilorin a ranar Juma’a, kwamandan rundunar NSCDC a Kwara, Bala Bawa Bodinga, ya ce rundunar za ta ci gaba da yaƙi da aikata laifuka tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike ko kuma a miƙa su ga wata hukuma  domin ci gaba da bincike,” in ji shi.

Ya kuma ce ana ci gaba da ƙoƙarin kamo wanda ya tsere, tare da gargaɗin masu aikata laifuka da su daina ko su fuskanci hukunci.

Haka kuma ya buƙaci al’umma su kasance masu lura tare da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *