AFCON 2026: Nijeriya Ta Ƙare A Matsayi Na Ɗaya A Rukunin C

[ad_1]

Daga Rabilu Sanusi Bena

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta zama kasa ta farko a gasar nahiyar kasashen Afirika ta bana da ta samu nasara a dukkan wasanni 3 da ta buga a matakin rukuni bayan lallasa kasar Uganda da ci 3-1 a wasansu na yau Talata.

Nijeriya ta hada maki 9 da kwallo 4 a wasanni 3 da ta buga, hakan yasa ta kare a matsayi na 1 a rukunin C na gasar, kasar Tunisia ce ke matsayi na 2 da maki 4 sai Tanzania da ta samu maki 2 a matsayi na 3 sannan kasar Uganda da ta kare a matsayi na 4 kuma na karshe da maki 1 kacal.

Paul Onuachu ne ya zurawa Nijeriya kwallonta ta farko a minti na 28 da fara wasa, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Raphael Onyedika ya zura kwallaye 2 rigis, wanda yayi sanadiyar samun nasarar Super Eagles din.

Yanzu Nijeriya za ta jira a kammala wasannin rukuni kafin ta san kasar da zata hadu da ita a zagayen 16 na sili daya kwale, Super Eagles na fatan lashe wannan gasar ta bana domin huce haushin rashin nasarar da sukayi a hannun Ivory Coast a wasan karshe na gasar na shekarar 2023.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *