Gidajen Sinima Na Sin Sun Tattara Kudade Yuan Biliyan 5 Bayan Nuna Fina-Finan Karshen Shekarar Nan
[ad_1]
Ya zuwa yau Lahadi 28 ga watan Disamban nan, fina-finan da aka nuna a karshen shekarar nan ta 2025 a gidajen sinima na kasar Sin, sun samar da kudaden shiga har yuan biliyan biyar, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 714, adadin da shi ne mafi yawa a kasar a makamancin lokaci, na shekaru takwas da suka shude.
Karsashin da fina-finan suka nuna ba kawai ya haifar da karin kudaden shigar gidajen sinima na kasar Sin zuwa sama da yuan biliyan 51 a shekarar ta 2025 ba ne, har ma ya shaida bunkasa, da tarin damammakin ci gaban kasuwar fina-finai ta kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link