Ta’addanci Ya Sa Fiye Da Mutun 300,000 Rasa Matsuguni A Neja – Bago

[ad_1]

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya bayyana cewar fiye da mutane 300,000 suka rasa wuraren zamansu a ƙannan hukumomi goma na Jihar saboda ci gaba da taɓarɓarewar tsaro da aka daɗe ana fama da shi, a Jihar.

Neja tana daga cikin Jihohin da lamarin ta’addanci na rashin tsaro yayi ma katutu, inda ƙungiyoyin ƴan ta’adda lokaci zuwa lokaci suna zuwa wuraren zama mutane da basu ji basu gani ba, suna karkashe mutane da garkuwa dasu,da suka haɗa da yara ƴanmakaranta.

Gwamna Bago Ya Gargadi ‘Yan APC Masu Yi Wa Jam’iyyar Zagon Kasa

Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago

Hare- haren ya kawo cikas ga yadda mutane suke suke neman yadda za su tafiyar da rayuwarsu, ya sa mutane da yawa yin ƙaura, hakan ya ƙara tsaurara rashin tsaro a ƙauyuka.

Sanadiyar hakan, iyalai da yawa yanzu suna zama cikin yanayin tsoro.An ƙauracewa gonaki saboda barazanar tashin hankalin, yayin da su kuma iyaye suka ƙagara su tura ‘ya’yansu zuwa makaranta.

Halin kai hare- haren ba kawai lamarin aikin noma ya shafa kaɗai ba, har ma da matsalolin raba kayan agaji a Jihar.

Da yake yi ma ƴanjarida jawabi ranar Asabar a Minna bayan da ya amshi kayan jinƙai daga gwamnatiun tarayya, Gwamna Bago ya bayyana yawan mutanen da suka rasa matsuguni a sanadiyar ci gaban da ake yi na kai farmaki a ƙananan hukumomin da abin ya shafata.

Ya ce“a yanzu, muma iya bada ƙiyasin, muna da fiye da mutane 300,000 da suka rasa wuraren zama a ƙananan hukumomi goma da abin ya shafa a faɗin Jihar Neja waɗanda suke fama da lamarin tsarin daya shafi tsaro,”.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin sa tana aiki da tuntuɓar gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro, saboda a samu damar dawo da zaman lafiya a wuraren da matsalolin suka fi shafa.

Ya bada tabbacin cewar yayin da hukumomin tsaro suka kawo taimako hakan zai sa waɗanda suka rasa wuraren zamansu su koma gidajensu domin ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *