Farashin fetur ya kai N1,080 kan kowace lita a Legas
[ad_1]
Farashin Litar Man Fetur ya ƙaru zuwa Naira 1,080 a wasu sassan Jihar Legas, sakamakon tashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Bincike ya nuna wasu gidajen mai a ranar Asabar sun fara sayar da man tsakanin Naira 1,020 zuwa Naira 1,080 kan kowace lita.
Ƙarin farashin ya biyo bayan ƙara kuɗin mai da matatar Dangote ta yi.
Farashin ya shafi masu ɗauko mai kai-tsaye daga matatar mai kafin su sayar wa jama’a.
Rahotanni sun ce matatar ta ƙara farashin zuwa Naira 995 kan kowace lita daga Naira 874, saboda tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
A yanzu haka ana sayar da gangar ɗanyen mai kusan dala 92.69 kan kowace ganga.
Farashin ɗanyen mai ya ƙaru ne saboda rikicin da ya ɓarke a yankin Gabas ta Tsakiya.
Masana harkar makamashi sun ce rikicin da ya shafi Amurka, Isra’ila da Iran na iya shafar samar da ɗanyen mai a duniya, wanda zai iya ƙara tashin farashin mai.
Masana sun kuma yi gargaɗin cewa idan farashin ɗanyen mai ya ci gaba da ƙaruwa, farashin man fetur a Najeriya na iya tashi har ya kai kusan Naira 1,100 kan kowace lita.
Bincike ya nuna cewa gidajen mai da dama sun riga sun ƙara farashin nasu.
A halin yanzu kuma, rahotanni daga Ibadan sun nuna cewa a wasu wurare ana sayar da man fetur a kan Naira 1,200 kan kowace lita.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link