Talauci Ne Ya Haifar Da Matsalolin Tsaro A Arewa – Gwamnan Jigawa
[ad_1]
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya ce talauci ne babban dalilin da ya haifar da matsalolin a Arewa.
Ya bayyana haka ne a Kaduna lokacin bikin cika shekaru 25 da kafa Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF).
Wannan ya fito ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar.
Gwamna Namadi ya ce ko da yake matsalar tsaro babbar barazana ce, dole a magance tushen matsalar, musamman talauci, ta hanyar amfani da tsare-tsaren tattalin arziƙi na dogon lokaci.
Ya bayyana cewa Arewa tana da albarkatun ƙasa, ƙasar noma, da ɗimbin ma’aikata.
Don haka, akwai damar kawar da talauci ta hanyar bunƙasa harkar noma.
A cewarsa, yawancin matsalolin tsaro suna da nasaba da talauci, kuma Arewa ba ta da hujjar ci gaba da kasancewa cikin talauci kasancewar tana da albarkatu da dama.
Saboda haka ne shugabannin Arewa ke himmatuwa wajen inganta noma.
Gwamnan ya yi imanin cewa gyare-gyaren da ACF, Gwamnonin Arewa, da Gwamnatin Tarayya ke goyon baya za su taimaka wajen sauya tsarin noma da farfaɗo da tattalin arziƙin yankin.
Ya ƙara da cewa bunƙasa noma zai samar da ayyukan yi da hanyoyin dogaro da kai ga miliyoyin mutane, kuma wajibi ne shugabanni su haɗa kai domin cimma wannan buri.
Gwamna Namadi ya taya ACF murna bisa cika shekaru 25 da kafuwa, sannan ya yaba da rawar da ta ke takawa wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaba a Arewa da Nijeriya baki ɗaya.
[ad_2]
Source link