Tinubu Ya Umarci A Tsaurara Tsaro A Dazukan Kwara, Neja Da Kebbi

[ad_1]


Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin inganta tsaro a dajin Jihar Kwara saboda yawaitar sace-sace da hare-haren ’yan ta’adda a kwanakin nan.

Ya kuma umarci Rundunar Sojin Sama ta ƙara sa ido ta sama a cikin dazukan da ake zaton ’yan ta’addan na ɓuya.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce wannan umarni ya shafi jihohin Neja da Kebbi.

Rundunar Sojin Sama za ta riƙa sintiri na awa 24 domin taimaka wa sojojin da ke ƙasa.

An kuma roƙi al’umma su riƙa sanar da jami’an tsaro duk wani abu da suke da shakku a kansa.

A makon da ya gabata ne, ’yan ta’adda suka sace sama da ɗalibai 300 da ma’aikata daga makarantar St. Mary’s da ke Neja.

Haka nan an sace ’yan mata 25 a Jihar Kebbi, da kuma masu ibada 38 daga wata coci a Jihar Kwara.

Kusan mutum 50 daga cikin waɗanda aka sace a St. Mary’s sun tsere, amma fiye da 265 har yanzu suna hannun ’yan bindigar.

Nijeriya na fama da matsalar garkuwa da mutane tsawon shekaru, ciki har da sace ɗaliban Chibok a 2014, inda har yanzu kimanin 90 ba a san halin da suke ciki ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *