Majalisa ta dakatar da kansiloli 4 kansiloli 4 a Kuros Riba

[ad_1]



Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba ta dakatar da wasu kansiloli huɗu na Ƙaramar Hukumar Akpabuyo na tsawon wata uku.

Majalisar ta dakatar da su ne bisa zargin aikata ayyuka yadda suke so da kuma nuna rashin biyayya ga dokoki.

Kansilolin da dakatarwar ta shafa su ne, Honarabul Innocent Meukpa  da Honarabul Patrick Eyo Elim da Honarabul Bassey Effiom Edem da kuma Honarabul Tete Oyoyo Ubene

Sakataren yaɗa labarai na shugaban majalisar dokokin, Matthew Okache, ya shaida wa wakilinmu cewa dakatarwar ta fara aiki ne nan take daga ranar 31 ga watan Maris, 2026.

Ana zargin kansilolin da yin watsi da ayyukan da ke gabansu tare da nuna halin ko-in-kula ga al’amuran ƙaramar hukumar.

A baya-bayan nan ma, majalisar dokokin Kuros Riba ta dakatar da Honarabul Idi Yakubu, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Ogoja, bisa zargin watsi da aikinsa da shiga sharholiya, lamarin da ya sa ya yi watsi da duk wasu ayyuka na ƙaramar hukumar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *