Gwamna Yusuf Ya Ziyarci Ƙananan Hukumomi 2 Kan Harin ‘Yan Bindiga A Yankunan

[ad_1]


Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a ranar Litinin, ya ziyarci kananan hukumomin Tsanyawa da Shanono na Jihar don duba yanayin tsaro bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kwanan nan a yankunan.

Gwamnan, wanda ya samu rakiyar shugabannin hukumomin tsaro a jihar da manyan jami’an gwamnati, ya bayyana hare-haren a matsayin “abin da ba za a yarda da shi ba,” yana mai tabbatar wa mazauna yankunan cewa, gwamnatinsa za ta dauki duk wani mataki da ya dace don kawo karshen wannan lamari.

Yayin da yake jawabi ga sojojin da aka tura yankunan da abin ya shafa, Gwamna Yusuf ya yi alkawarin cikakken goyon bayan gwamnatin jihar ga jami’an tsaro, gami da samar da walwala, kayayyaki da duk wani kayan aiki da ake bukata don dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi.

Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a lokacin hare-haren kuma ya bayyana fatan cewa, wadanda ke tsare a hannun maharan, za a kuɓutar da su nan ba da jimawa ba.

A cewar gwamnan, gwamnatinsa ta ci gaba da jajircewa wajen yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a cikin al’ummomin da abin ya shafa da kuma fadin jihar baki ɗaya

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *