Sin Ta Ce Ficewar Amurka Daga Hukumomin Kasa Da Kasa 66 Ba Sabon Abu Ba Ne

[ad_1]

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fada a yau Alhamis cewa matakin da Washington ta dauka na janyewa daga hukumomin kasa da kasa 66, wadanda suka kunshi hukumomi 31 na Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyi 35 wadanda ba na MDD ba, ba sabon abu ba ne, tana mai jaddada cewa an kafa cibiyoyin mu’amalar mabambantan bangarori ne don biyan bukatun dukkan kasashe na bai-daya maimakon fifita muradun wata kasa daya tilo.

A wani taron manema labarai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, halin da duniya ke ciki a yanzu ya sake nuna cewa ingantaccen tsarin mu’amalar mabambantan bangarori ne kawai zai iya hana yaduwar tsarin rayuwar namun daji na mai karfi ya buge mai rauni, da kuma hana tsarin kasa da kasa fadawa cikin mamayar siyasar nuna karfin iko da amfani da karfi, wadda ta ce yana da matukar muhimmanci ga kananan kasashe da kuma kasashe masu tasowa.

A martanin da ta mayar kan kwace wani jirgin ruwan mai dauke da tutar Rasha da sojojin Amurka suka yi a Arewacin Tekun Atlantika, Mao ta yi nuni da cewa kwace jiragen ruwan kasashen waje ba bisa ka’ida ba da Amurka ta yi a yankin ruwa na kasa da kasa ya saba wa dokokin kasa da kasa, kuma kasar Sin tana ci gaba da nuna adawa da kakaba haramtaccen takunkumi na gaban-kai wanda ba shi da asali a cikin dokokin kasa da kasa kuma bai samu izini daga kwamitin sulhun MDD ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *