Ƙungiyar Kwankwaso National Network Ta Gudanar Da Taron Kudu Maso Yamma A Ibadan
[ad_1]
Kwankwaso National Network (KNN) ta shiyyar Kudu maso Yammacin Nijeriya ta gudanar da wani muhimmin taron tattaunawa a ranar Talata, 6 ga Janairu, 2026, a birnin Ibadan na jihar Oyo. Taron ya samu halartar manyan jami’an shugabancinn kungiyar na kasa, ciki har da Babban Mai Kula da KNN na kasa, Asiwaju Mashood Shittu, mai kula da shiyyar Kudu maso Yamma, Hon. Daniel Solomon, tare da dukkan masu kula da jihohi shida na yankin.
Mataimakin Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na KNN, Abubakar Guda Musa, ya bayyana cewa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taka wajen amfani da mukamansa a gwamnati domin inganta rayuwar ’yan Nijeriya, musamman marasa karfi. Ya bayyana Kwankwaso a matsayin shugaba na musamman, yana tunatar da irin nasarorin da ya samu a matsayinsa na tsohon gwamnan Kano da kuma Ministan Tsaro.
- Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
- Zan Sauya Sheka In An Bani Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa Ko Mataimaki – Kwankwaso
Asiwaju Mashood Shittu ya jaddada gagarumar gudunmawar Kwankwaso a fannin ilimi, inda ya ce a zamanin gwamnatinsa a Kano an samar da kayan makaranta kyauta, da ciyarwa ga dalibai a kullum, tare da ilimi kyauta daga matakin firamare zuwa jami’a. Ya kara da cewa sama da matasa 4,000 aka dauki nauyin karatun su zuwa kasashe fiye da 14 a ketare, yayin da dubban dalibai suka samu tallafin karatu a manyan jami’o’i a cikin Nijeriya. Ya kuma bayyana Kwankwaso a matsayin “Awolowo na wannan zamanin” da jagora mai tafiya da akidar marigayi Malam Aminu Kano.
A bangaren tsaro, an tuna rawar da Kwankwaso ya taka a matsayinsa na Ministan Tsaro, musamman wajen kawo sauye-sauye a tsarin biyan albashin sojoji ta hanyar amfani da fasahar zamani, lamarin da ya inganta walwalar jami’an tsaro. Hon. Daniel Solomon ya bayyana taron a matsayin tunatarwa kan muhimmancin shiga harkokin dimokuradiyya, yayin da shugabannin jihohi shida na KNN a yankin suka sha alwashin kara karfafa tafiyar Kwankwasiyya a Kudu maso Yamma. Taron ya kammala cikin lumana da nishadi daga mahalarta.
[ad_2]
Source link