Jam’iyyar APC Ta Ribas Ta Yi Watsi Da Matakin Tsige Gwamna Fubara

[ad_1]

Jam’iyyar APC reshen jihar Ribas ta yi watsi da kudirin da Majalisar Dokokin Jihar ta shigar kan Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, tana mai gargaɗin cewa irin waɗannan matakai na iya kawo cikas ga zaman lafiyar jihar.

A cikin wata sanarwa da Kakakin APC na jihar Ribas, Darlington Nwauju, ya fitar a ranar Alhamis, jam’iyyar ta nuna damuwa kan “abin takaici” da ke faruwa a Majalisar, inda ta amince da rawar da majalisar ke takawa a matsayinta na ɗaya daga cikin ginshiƙan gwamnati mai zaman kansa wanda ke da alhakin kafa dokoki amma yunƙurin tsige gwamna bai dace ba kuma ba zai yiwu ba.

  • Komai Nisan Dare Gari Zai Waye
  • Gwamnatin Tarayya Ta Biya ‘Yan Wasan Super Eagles Haƙƙoƙinsu

APC ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin rikice-rikicen cikin gida ne kawai na Jam’iyyar PDP, wanda har yanzu ba a warware su ba, don haka, ta yi gargaɗin cewa, bai kamata waɗannan batutuwa su zamo barazana ga zaman lafiyar gwamnatin da APC ke jagoranta a jihar Ribas ba.

Jam’iyyar ta danganta barazanar tsige gwamna Fubara kan rashin jituwa a kasafin kudlɗi, tana mai jayayya cewa irin waɗannan batutuwa ba sa buƙatar tsauraran matakan majalisa kamar tsige gwamna.

Tun da farko, LEADERSHIP ta ruwaito cewa a zaman da aka gudanarwa a ranar Alhamis, Majalisar Dokokin Jihar ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Martins Amaewhule, ta fara zaman tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu bayan ta gabatar da jerin zarge-zargen aikata manyan laifuka a kan su biyun.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *