Yadda aka yi asara a gobarar da ta ƙone shaguna sama da 10 a kasuwar Tatari Ali a Azare

[ad_1]



Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar Abubakar Tatari Ali da ke garin Azare a Jihar Bauchi, ta ƙone shaguna sama da 10, lamarin da ya kai ga tafka asara mai tarin yawa.

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Juma’a.

Har yanzu ba a gano ainihin abin da ya haddasa gobarar ba, sai dai wasu na zargin cewa wutar lantarki ce ta jawo lamarin.

Shaidu sun ce gobarar ta fara ne a sashen sayar da yadudduka da hijaban mata a kasuwar.

Wutar ta ci gaba da ci na wasu sa’o’i kafin jami’an kashe gobara su isa domin shawo kan lamarin.

An ce kafin jami’an kashe gobara su isa, gobarar ta riga ta yi ɓarna mai yawa tare da ƙone shaguna da dama a kasuwar.

Sarkin Katagum, Umaru Muhammad Kabir Umar, ya kai ziyara kasuwar domin jajantawa ’yan kasuwar da abin ya shafa.

Ya yi musu addu’ar Allah Ya mayar musu da abin da suka rasa, sannan ya yi alƙawarin kai rahoton lamarin ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni domin a tallafa musu.

Haka kuma wakilan ƙaramar hukumar Katagum sun ziyarci kasuwar domin jajanta wa ’yan kasuwar.

Ɗaya daga cikin shugabannin kasuwar, Malam Habu Salisu, ya ce gobarar koma baya ce ga ’yan kasuwar, musamman waɗanda shagunansu suka ƙone.

Ya ce a binciken farko, shaguna kusan 10 sun ƙone ƙurmus ba tare da an iya ceton komai ba, yayin da wasu shagunan kuma wutar ta taɓa su kaɗan kafin a samu nasarar kashe ta.

Wani ɗan kasuwa, Malam Aminu, ya ce jami’an kashe gobara, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun taimaka wajen kashe gobarar da kuma kare kayayyakin mutane daga ɓarayi.

Kawo yanzu dai ba a tantance yawan asarar dukiyar da aka yi ba.

Sai dai ba a samu asarar rai a gobarar ba, duk da cewa kayayyaki da dama sun ƙone.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *