Sauya Sheƙa: Gwamnan Kano zai gana da Tinubu a Faransa

[ad_1]



Rahotanni na cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ya shirya wata ganawa da Shugaba Bola Tinubu gabanin tsayar da matsaya dangane da batun sauya sheƙar zuwa jam’iyyar APC.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wannan ganawar na zuwa ne bayan wata ganawar sirri da gwamnan ya yi da madugun Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Bayanai na cewa, gwamnan ya yi ganawar sirri da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Miller Road a Kano, gabanin tafiyarsa ƙasar Faransa inda a can ake kyautata zaton zai gana Shugaba Tinubu.

Har wa yau, rahotanni na cewa ganawar da Kwankwaso ta gudana ne da tsakar dare, inda ake zargin gwamnan ya kai wa ziyara a ƙoƙarin shawo kan ubangidansa domin ya biyo sahunsa zuwa jam’iyyar APC, kamar yadda Shugaba Tinubu ya buƙata.

Sai dai alamu sun nuna cewa haƙar gwamnan ba ta cimma ruwa ba, domin washegarin ganawar, Kwankwaso ya bayyana wa magoya bayansa cewa ba shi ɗan siyasa ne da ba zai sayu da kuɗi ba, yana mai sukar salon mulkin APC musamman kan sha’anin tsaro da tattalin arziƙi.

Majiyoyi sun ce yunƙurin Gwamna Abba na sauya sheƙa na fuskantar ƙalubale sakamakon martanin jama’a a Kano, inda yawancin magoya bayan jam’iyyarsa ta NNPP ke ci gaba da mara wa Kwankwaso baya, duk da cewa wasu ’yan majalisa da shugabannin ƙananan hukumomi na komawa APC.

Rahoton na Daily Nigerian ya ce manyan shugabannin APC na Kano na bibiyar lamarin sannu a hankali, yayin da ake ganin Kwankwaso na samun ƙarin goyon baya daga al’umma, lamarin da ka iya shafar makomar siyasar gwamnan idan ya koma APC.

Majiyoyi sun ƙara da cewa Gwamna Abba zai shelanta wa Shugaba Tinubu yadda ganawarsa da Kwankwason ta kasance, kafin yanke shawarar ƙarshe kan sauya sheƙa, bayan tuntuɓa da shugabannin APC na jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *