Hukumar Kula Da Alkalai Ta Haramta Wa Lauyoyi 34 Zama Masu Shari’a A Nijeriya
[ad_1]
Idris Aliyu Daudawa
Lauyoyi 34 wadanda aka bada sunayensu domin su zama Alkalai ko masu shari’a na babbar kotun tarayya aka gano cewa basu mallaki muhimman abubuwan da ake bukata ba ace an mallake su kafin a kai ga basu mukaman da aka yi niyya, da akwai dai babbar bukata da ita gaskiya ce kafin mutum ya kasance ya cancanci zama a Benci kan lamarin daya shafi shari’a ta kasa.
An gane hakan ne cikin rahoton da hukumar harkokin shari’a ta kasa wadda ita ce ta yi wa Lauyoyi 62 jarrabawa wadanda aka zaba bada dadewa ba, za’a nada su kan mukaman Alkalai ko kuma masu shari’a na Babbar kotun tarayya.
- Batutuwan Da Suka Ci Wa ‘Yan Adawa Tuwo A Ƙwarya A Siyasar 2025
- Sama Da Kwantainoni 600 Ke Sauka Duk Wata A Defo Din Kano —Mahukunta
Kamar yadda majiyar ta mu ta bayyana su Lauyoyin 62 a wasu watannin da suka gabata sun samu nasarar lashe jarrabawar CBT da Babbar kotun tarayya ta jagoranci yi, saboda haka ne sai aka sake ba ita hukumar sunayensu domin su sake fuskantar bincike da kuma ganawa tsakaninsu da (NJC).
Majiyar ta ce idan aka yi amfani da sabon tsari na kamar yadda hukumar ta tanadar a karkashin jagorancin Babbar mai shari’a ta Nijeriya (CJN),Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta ce a tabbatar da duk wadanda za’a basu wadancan mukaman a tabbatar da suna da gaskiya, cancanta, mutane kuma masu gaskiya da rikon amana, sune aka nada a mukaman jami’an shari’a,shi ya sa aka dauki matakin da sai al’umma sumn amince da su.
“Sai aka gaiyaci wasu mutane su tofa albarkacin bakinsu akan su mutanen da suka samu nasarar lashe jarabawar’akwai kuma abubuwan da aka bukata wadanda sai mutum ya tsallakesu ne za’a fara tunanin ba shi mukamin, sun hada da lamarin gaskiya, yadda mutumin yake tafiyar da harkokinsa, da kuma cancanta akan matsayin ko mukamin da aka ce za’a ba shi ko bata,” majiyar tace cikin bayanin da ta yi, gaiyatar tana dauke cikin wata takardar da,aka wallafa ranar 17 ga Satumba 2025.
Bayanan da mutanen suka yi abi akwai bada kwarin gwiwa kan matakin da ya kamata a dauka, sai dai kuma ya yi sanadiyar cire sunayen Lauyoyi mutane 34 da aka gano cewar basu cancanta a nadasu su kasance masu shari’a ko Alkalan Babbar kotun tarayya ta kasa.
A daya daga korafe- korafen da aka amsa da ke daukae da sa ranar 22 ga Satumba 2025, amma an amshi takardar ranar 23 ga Satumba,da babban Sakataren hukumar FJSC, ya samu dangane da daya daga cikin wadanda aka bada sunayensu,ma’aikaciya ce daga Jihar Imo, da aka yiwa zargiun cewar ta cika son amsar na goro wato Rashawa da cin Hanci”,”saboda sha’awart da take da ita, ta amshi cin Hanci”.
Mutumin da ya rubuto korafin,wanda yace shi abin ya shafe shi saboda wani rusau din da ya hada da kaddarasa ta muhalli wato gida a Abuja, inda ya yi zargin ba kawai an kama shi bane wanda ‘yansanda suka yi,dangane da rushe ma shi muhalli,sai ma da aka tilasta ma shi ya bada Naira milyan daya kafin a sake shi kan sharadin beli.
Yayin da yake yin kira da hukumar kula harkokin shari’a ta yi watsi da sunanta, wanda ya rubuta korafin cewa ya yi halin wadda aka bada sunan nata “a takaice dai ana iya cewa ita mace da bata da gaskiya, gaba daya duk lamurranta sun nuna akwai gazawa kan gwajin da aka yi mata kan irin kimarta, kai bata na cancanta a nada ta ba a matsayin mai shari’a ta babbar kotun tarayya ta Kasa”.
Ya kara da cewa: “Shi ma bangaren na shari’ar yana da na shi laifin a gaban al’umma, amma duk da haka suna maraba da matakin da bangaren shari’ar ya dauka wajen tsaftace bangaren daga masu halayen karbar Rashawa da cin Hanci, masuu kuma son kowane lokace su kaucewa inda gaskiya take saboda hakan.”
Da aka tuntube ta, darekatar labarai, ta hukumar NJC,Mrs Kemi Ogedengbe, wadda ta ki ta ce ko uffan,sai dai ta yi bayani dnagane rashin gaskiya na yawancin wadanda aka bada sunayen nasu, amma duk da hakan ta ce hukumar za ta yi taro tsakanin 13 zuwa 14 ga Janairu 2026 domin ta amince ma wadanda suka cancanci, a nada su kan mukaman na Alkalai masu shari’a na babbar kotun tarayya ta kasa.
Duk da hakan ta ce Lauyoyi 28 da aka amince da su za su sake fuskantar yin wani bincike akan su, domin a gano cancantarsu, ta yikarin haske mai nuna hukumar NJC ta shirya tsaf domin ta rage mizanin cancantar samun mukamin ba tare da yin la’akari da kowane ne abin ya shafa ba.
[ad_2]
Source link