Gwamnatin Tarayya Ta Ci Amanar ‘Yan Nijeriya Bayan Sauya Dokokin Haraji – Atiku
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, kuma jigo a ADC, Atiku Abubakar, ya ce sauye-sauyen da aka samu a dokokin haraji da takardun da aka sanya hannu a kansu cin amanar ‘yan ƙasa ne, kuma ya saɓa wa kundin tsarin mulki.
Atiku, ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce sauyin ya nuna cewa gwamnati ta fi mayar da hankali kan tara kuɗaɗe daga jama’a fiye da kula da buƙatunsu.
- Najeriya Na Da Wata Kawa Mai Sanin Ya Kamata
- APC Za Ta Karɓi Gwamnan Filato A Watan Janairun 2026
Jigon siyasar ya yi kira da a dakatar da aiwatar da sabbin dokokin harajin da ake sa ran farawa a watan Janairun 2026 domin a gudanar da cikakken bincike.
Ya kuma buƙaci majalisar dokoki ta gyara sauye-sauyen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, a hukunta masu hannu, sannan hukumar EFCC ta gudanar da bincike kan lamarin.