Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ta Tura Tawaga Ziyara A Turai

[ad_1]

Daga ranar 23 zuwa ta 29 ga watan Maris da muke ciki, ma’aikatar tsaron kasar Sin ta tura wata tawaga zuwa nahiyar Turai, don ziyartar kungiyar kasashen Turai ta EU, da hedkwatar kungiyar tsaro ta NATO, gami da kasar Switzerland. Inda jami’an kasar Sin da takwarorinsu na kasashen Turai suka gudanar da taron tattaunawar hukumomin tsaro na Sin da kungiyar EU karo na 15, da na tattaunawar kasar Sin da kungiyar tsaro ta NATO kan manufofin tsaron kasa karo na 9, gami da taron ma’aikatun tsaron kasashen Sin da Switzerland karo na 15, don musayar ra’ayoyi kan batutuwan da ke jan hankulansu, musamman ma wadanda suka shafi yanayin tsaro na wasu shiyyoyi, da na duniya baki daya. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *