NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
[ad_1]
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025.
Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci.
Shugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696.
Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar.
Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba.
Sai dai an dakatar da sakin sakamakon makarantu takwas a Ƙaramar Hukumar Lamorde ta Jihar Adamawa saboda rikicin ƙabilanci da ya auku tsakanin 7 zuwa 25 ga watan Yuli, 2025.
Rikicin ya yi sanadin wanda ya hana zana jarabawar darusa 13 da takardu 29.
Hukumar na tattaunawa da gwamnati don sake bai wa ɗaliban damar rubuta jarabawar.
NECO ta kuma bayyana cewa an samu makarantu 38 daga jihohi 13 ds laifin aikatar satar amsa yayin zana jarabawa.
Za a gayyace su zuwa babban ofishin NECO kafin ɗaukar mataki a kansu.
Haka kuma, hukumar ta dakatar da mutum tara da ke aikin sanya ido sake kula da jarabawa saboda gazawarsu wajen hana satar amsa.
Mutanen da aka dakatar, uku sun fito daga Jihar Ribas, uku daga Babban Birnin Tarayya, da kuma mutum ɗai-ɗai daga Jihohin Neja, Kano da Osun.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link