An Kai Harin Haɗin Gwuiwa Ne Kan Ƴan Ta’adda Ba Da Manufar Hari Kan Addini Ba – Bwala
[ad_1]
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa harin sama da aka kai a Jihar Sokoto a ranar Alhamis haɗin gwuiwa ne tsakanin Nijeriya da Amurka, kuma ba a kai shi ne bisa ƙabilanci ko addini ba, sai dai kan ’yan ta’adda.
Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin sadarwa Daniel Bwala, ya yi wannan ƙarin haske ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce harin ya samo asali ne daga makonni na haɗin kai, da musayar bayanan sirri da kuma sa ido tsakanin ƙasashen biyu.
- Tinubu Ba Zai Tattauna Da ’Yan Ta’adda Ba — Bwala
- Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
Bwala ya jaddada cewa Nijeriya ta taka muhimmiyar rawa musamman wajen samar da bayanan sirri da daidaita matakan aikin kafin da bayan harin, yana mai cewa wannan na daga cikin ci gaba da ake yi domin kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar.
Ya ƙara da cewa ya kamata kada a fassara harin a matsayin wanda aka kai kan wata ƙabila ko addini, yana mai jaddada cewa abin da gwamnati ke mayar da hankali a kai shi ne fatattakar masu aikata laifuka kaɗai.
[ad_2]
Source link