Masana Sun Bayyana Yadda Kasafin Kudin 2026 Zai Shafi Tsaro Da Ilimi Da Kiwon Lafiya
[ad_1]
A yayin da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2026, al’ummar kasa na fatar ganin an aiwatar da dukkanin ayyukan da aka tsara ba tare da watsi da mafi yawan alkawuran da gwamnati ta daukar wa jama’a ba.
Kasafin kudin shekara- shekara shi ne alkiblar kowace irin gwamnati wajen tafiyar da harkokin mulki, bunkasa tattalin arziki, inganta rayuwar al’umma, wadata kasa da abinci, kawar da matsalolin tsaro da samar da abubuwan more rayuwa.
- Yawaitar Garkuwa Da Manoma Na Iya Haifar Da Karancin Abinci A 2026 —Bincike
- Jam’iyyar NNPP Za Ta Yi Gagarumin Tasiri A Zaben 2027 – Kwankwaso
A kowace shekara, al’ummar Nijeriya na sa ido da fatar ganin kudurorin da aka tsara a kasafin kudi za su wuce rubutu a takarda su koma ayyukan zahiri da ke shafar rayuwar jama’a kai tsaye.
Duk da yawan kasafin kudin da ake gabatarwa da alkawuran da ke tattare da su, babbar fata da bukatar al’umma ita ce ganin an aiwatar da kasafin kudin kashi 100 cikin 100, domin kudaden da aka ware su kai ga inda ake bukata ba tare da tangarda ko jinkiri ba.
A na kallon cikakken aiwatar da kasafin kudi a matsayin ma’aunin gaskiya da ingancin shugabanci, musamman a lokacin da kasa da al’ummar ta ke fuskantar kalubalen tattalin arziki, gawurtacciyar matsalar tsaro da zamantakewa.
A wannan yanayi, kasafin kudi ba wai kawai takarda ce ta kididdiga ba, illa alkawari ne tsakanin gwamnati da al’umma wanda aiwatar da shi yadda ya kamata zai zama ginshikin gina amincewa, samar da ayyukan yi da tabbatar da ci- gaba mai dorewa ga al’ummar Nijeriya bakidaya.
A yayin da ShugabaTinubu ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2026 a makon jiya wanda ya kama naira tiriliyan 58.18, a gaban zaman hadin gwiwa na Majalisar Tarayya ya bayyana tsare- tsaren kudaden gwamnati da suka ta’allaka kan farfado da kasa, tabbatar da daidaito da gina ci- gaba mai dorewa.
Kasafin kudin.wanda aka tsara bisa ajandar gwamnati ta bunkasa kasa ya ba da fifiko ga ginshikai hudu masu muhimmanci da ake ganin su ne tubalin ci- gaban kasa, wato tsaro, ilimi, kiwon lafiya da kuma ababen more rayuwa kamar yadda ya bayyana a ranar Juma’a.
A cewar Shugaban Kasa, wadannan sassa suna da alaka da juna, kuma su ne ginshikin wanzuwar Nijeriya wajen cimma ci- gaban da zai shafi kowa da kowa, fadada tattalin arziki da kuma daidaiton zamantakewa.
“Wadannan muhimman sassa suna da alaka da juna. Idan babu tsaro, zuba jari ba zai yi wu har ya bunkasa ba, idan babu ilimi da lafiyayyar al’umma aiki ba zai gudana ba. Haka ma idan babu ababen more rayuwa, ayukan yi da kasuwanci ba za su bunkasa ba. Wannan ne ya sa aka tsara wannan kasafin kudi a matsayin tsari guda mai ma’ana na sabunta kasa baki daya.” Ya bayyana.
Kasafin kudin shekarar 2026 ya tanadi jimillar kudaden shiga na naira tiriliyan 34.33, yayin da jimillar kudaden gudanarwa suka kana naira tiriliyan 58.18, abin da ya haifar da gibin kasafi na naira tiriliyan 23.85 wanda ke wakiltar kashi 4.28 cikin 100 na jimillar arzikin kasa a ma’aunin GDP.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewar an gina wadannan hasashe ne bisa kimantawa da taka- tsantsan inda aka dauki farashin gangar danyen mai a kan dala 64.85 da hasashen samar da ganga miliyan 1.84 a kowace rana tare da canjin kudii na naira 1, 400 zuwa dala daya ta Amurka.
Gwamnatin tarayya ta yi hasashen gudanar da manyan ayyuka da naira tiriliyan 26.08, yayin da kudaden yau da kullum (ba na bashi ba) suka kai naira tiriliyan 15.25.
A cewar Shugaban Kasa, wadannan alkalumma na nuna kudurin gwamnatin sa wajen daidaita tsantseni a harkar kudaden gwamnati da kuma gaggawar bukatar zuba jari domin habaka ci- gaban tattalin arziki.
Fannin Tsaro
A cikin kasafin kudin shekarar 2026, bangaren tsaro da kariya ne ya samu kaso mafi girma na musamman inda aka ware naira tiriliyan 5.41. Wannan a cewar gwamnatin na nuni da muhimmancin da ake bai wa kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa tsaro ne tubalin bunkasar tattalin arziki da daidaiton zamantakewa a kowace kasa don haka gwamnatin sa ba za ta yi kasa a guiwa wajen sauke nauyin da ke kan ta ba.
Ya ce gwamnatin tarayya ta fara cikakken sake fasalin tsarin tsaron kasa ta yadda aka mayar da hankali kan sabunta ayyukan tsaro bisa bayanan sirri da kuma amfani da fasahar zamani wajen sa- ido da leken asiri.
Shugaban ya kuma bayyana cewa kasafin kudin ya tanadi kudaden musamman domin karfafa rundunar soji, fadada yawan jami’ai da kuma sayo sabbin kayan aiki da manyan na’urori na zamani domin tunkarar sabbin barazanar tsaro da ke addabar kasa.
Wani muhimmin ginshiki a cikin wannan shiri shi ne aiwatar da sabon tsarin kasa na yaki da ta’addanci wanda aka tsara domin tunkarar ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka na tashin hankali cikin inganci da kwarewa.
Shugaba Tinubu ya ce wannan sabon tsari na nuni da cikakken sake fasalin na’urorin tsaro kasa, wanda ya ta’allaka ne kan umurni guda, hadin gwiwar bayanan sirri, kwanciyar hankalin al’umma da dabarun yaki da ‘yan tawaye.
“Za mu zuba jari a bangaren tsaro tare da cikakken tsarin tabbatar da nasara ko akasin ta domin duk kudin da aka kashe a tsaro dole ne su haifar da sakamakon tsaro na ainihi.
A karkashin sabon tsarin tsaron, duk wata kungiya ko mutum mai dauke da makami da ke aiki ba tare da izinin gwamnati ba, a na daukar sa a matsayin dan ta’adda.
Wannan ya hada da ‘yan ta’adda, gungun masu daukar makamai, kungiyoyin asirin da ke tayar da tashin hankali, mayakan da ke fakewa a dazuka da kuma sojojin haya daga kasashen waje.
Haka kuma, duk wanda ya taimaka ya dauki nauyi, ya ba da mafaka ko ya mara wa irin wadannan kungiyoyi baya, ciki har da ‘yan siyasa, shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya da shugabannin addini, za a dauke su a matsayin ‘yan ta’adda.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa wannan kakkarfan shirin an tsara shi ne domin kawar da rudani, rufe kofofin uzuri da tabbatar da cikakken alhaki da gaskiya a dukkan ayyukan tsaro na kasa.
Ilimi Da Lafiya
Baya ga sha’anin tsaro, kasafin kudin 2026 ya ba da fifiko sosai kan ci-gaban rayuwar al’umma domin kuwa gwamnati ta ware naira tiriliyan 6 ga fannonin ilimi da kiwon lafiya ta yadda naira tiriliyan 3.52 aka kebewa sha’anin ilimi, yayin da naira tiriliyan 2.48 aka tanadarwa kiyon lafiya.
A fannin ilimi, gwamnati ta fadada damar samun shiga manyan makarantu da jami’o’i ta hanyar shirin tallafin bashin karatu, wanda ya tallafa wa dalibai sama da 418,000 tare da hadin gwiwar manyan makarantu 229 a fadin kasa.
Shugaba Tinubu ya ce, kudaden za su tallafa wajen habaka sana’o’i saboda alakar da ke tsakanin kwarewa, samun aiki da kuma habaka ayyukan yi a matakin kasa.
Zuba jari a fannin lafiya, wanda ke wakiltar kimanin kashi 6 cikin 100 na jimillar kasafin kudi, an tsara shi ne domin karfafa kayan aikin kiwon lafiya, fadada damar samun kulawa daga cibiyoyin kiyon lafiya a matakin farko da manyan asibitoci da kuma rage yawan cututtuka a fadin kasa.
Shugaba Tinubu ya jaddada batun tattaunawa da Gwamnatin Amurka a baya-bayan nan wadda ta samar da sama da dala miliyan 500 a matsayin tallafin kudi domin bunkasa wasu shirye- shiryen kiwon lafiya na musamman a Nijeriya.
Ya tabbatar da cewar za a yi amfani da kudaden cikin gaskiya da bayyana yadda ake kashe su domin inganta sakamakon kiwon lafiya da kuma karfafa hadin gwiwa domin ci- gaba mai dorewa.
Abubuwan More Rayuwa
Bunkasa ababen more rayuwa da habaka tattalin arziki sune ginshiki na uku a cikin kasafin kudin shekarar 2026 inda aka tanadi naira tiriliyan 3.56.
A fannin noman abinci, Shugaba Tinubu ya jaddada mahimmancin alakar da ke tsakanin samar da abinci da tsaron kasa. A cewar sa kasafin kudin ya ba da fifiko ga tallafin kayan aiki da injuman noma, tsarin ban ruwa da ya dace da sauyin yanayi da kuma habaka wuraren ajiya, sarrafawa da kimar kayan gona.
Wadannan matakan an tsara su ne domin rage asarar amfanin gona bayan girbi, kara kudin shiga ga kananan manoma da zurfafa masana’antar sarrafa kayan gona.
Ta hanyar karfafa kasuwannin abinci da kimar kayan gona, gwamnati na sa ran habaka karfin tattalin arzikin Nijeriya da rage dogaro da shigo da kaya daga waje.
“Wadannan matakan za su rage asarar amfanin gona bayan girbi, inganta kudin shiga ga kananan manoma, zurfafa masana’antar sarrafa kayan gona tare da gina tattalin arziki mai dorewa da nagarta.” Ya bayyana.
Ra’ayin Masana
Masu fashin bakin lamurran yau da kullum na nuna damuwa kan yadda har yanzu ba a aiwatar da wasu sassa na kasafin kudin shekarun 2023 da 2024 ba. A cewar su fayyace ayyukan gwamnati kafin gabatar da sabon kasafin kudi yana da matukar muhimmanci.
A cewar su rashin aiwatar da tsohon kasafin kudin shekarun 2023 da 2024 da suka gabata na iya janyo rudani, rashin amincewa da rage tasirin sabbin tsare-tsaren tattalin arziki. Haka kuma, idan ba a fayyace ayyukan da aka ayyana ba, sabon kasafin kudi na iya zama mai wahalar tantancewa da bin diddigi wanda hakan zai rage tasirin kudaden da ake kashewa wajen ci- gaban kasa.
Saboda haka a ra’ayin masana bayyana dukkanin ayyukan gwamnati da cikakken rahoto kan yadda aka aiwatar da tsofaffin kasafin kudi zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya, ingantaccen tsari da karfafa amincewar al’umma a duk lokacin da ake shirin gabatar da sabon kasafi.
[ad_2]
Source link