An Kashe Wani Mutum Saboda Cajar Wayar Hannu A Anambra
An kashe wani matashi mai suna Chisom, sanadin fada akan cajar wayar hannu a Ihiala, Jihar Anambra.
PUNCH Metro ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Disamba bayan wata takaddama tsakanin shi da dan uwansa wanda har yanzu ba a gano sunansa ba.
- Harin Bam A Masallacin Borno Aiki Ne Na Rashin Imani — Ministan Sufuri
- Jam’iyyar NNPP Za Ta Yi Gagarumin Tasiri A Zaben 2027 – Kwankwaso
A cewar wani rubutu da aka gani a dandalin wayar da kan jama’a kan yaki da kungiyoyin asiri, Confra Naija, a ranar Talata, Chisom ya taba bayar da cajin wayar ga dan uwansa a baya.
Sai dai rikici ya barke lokacin da Chisom ya tafi daukar cajin wayar, wanda daga bisani ya rikide zuwa fada mai tsanani. A yayin wannan fada, an zargi dan uwansa da yankan Chisom wurare da dama.
Dandalin ya kara da cewa, mahaifin wanda ake zargi, wanda shi Baffan Chisom ne, kuma ya farmake shi, lamarin da ya kai ga mutuwar Chisom.
Rubutun ya ce: “A Ihiala, wani matashi mai suna Chisom ya kashe shi dan uwansa wanda ba mamba ne na kungiyar asiri ba, saboda sabani kan cajin wayar hannu.”
“An ce Chisom ya ba dan uwansa cajin wayar, daga bisani sai ya tafi karba, amma rikici ya barke, inda dan uwansa ya yanke shi da wuka wasu wuarare da dama a yayin fadan.”
Dandalin ya kara da cewa an kama dan uwan nasa a baya, yayin da matasa a cikin al’umma suka kona gidan Baffan nasa.
A cikin wani bidiyo da wakilinmu ya gani, an ga gawar mamacin kwance a gadon asibiti yayin da ‘yan uwansa ke kuka.
Kokarin samun martani daga Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yansandan Jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, bai yi nasara ba, saboda bai amsa kiran waya ba. kazalika bai amsa sakon kar-ta-kwana da aka tura masa ba ba har lokacin kammala wannan rahoto.
Takaddama tsakanin ‘yan uwa sau da yawa tana rikidewa zuwa tashin hankali mai kisa a wasu sassa na jihar. Wadannan sun hada da sabani kan kadarori, kudi, da sauran al’amuran sirri, wanda sau da yawa ke karewa da jini.