Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Adawar Al’ummun Duniya Da Farfado Da Matakan Amfani Da Karfin Soji
[ad_1]
Kalaman baya bayan nan da firaministar Japan ta furta dangane da yankin Taiwan na Sin, sun sha suka da Allah wadai daga sassan kasa da kasa.
Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta gudanar, ya nuna yadda kaso 87.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin suka nuna matukar bukatar Japan ta gaggauta janye kalaman tayar da husuma, suna masu kira ga daukacin kasashen duniya da su dunkule waje guda, don nuna adawa da duk wani yunkuri na farfado da salon amfani da karfin soji.
Kazalika, kaso 88.3 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin kalaman takalar yaki na firaministar Japan, sun yi matukar keta kundin tsarin mulkin Japan, sun kuma yi matukar illata kima da mutuncin Japan a idanun duniya.
Kafar CGTN ta wallafa kuri’un jin ra’ayin jama’ar nata ta harsunan Turancin Ingilishi, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci da harshen kasar Rasha, inda jimillar masu bayyana ra’ayoyi 4,549 suka bayyana mahangarsu cikin sa’o’i 12. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link