Tsarin ‘Digital Call-Up’ Ta NPA Ya Samu Karɓuwa A Tashar Jiragen Ruwa Na Onne
[ad_1]
Direbobin manyan motoci da ke dakon kaya a tashar jiragen ruwa ta Onne, a Jihar Ribas, sun bayyana cikakken goyon baya da farin ciki ga sabon tsarin da hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) ta ɓullo da shi.
Tsarin na ‘Electronic Call-Up System’, wanda yake amfani da fasahar zamani wajen tantance motocin da ya dace a bai wa jigilar kaya a lokaci, an tanade shi ne da nufin rage cunkoson motocin dakon da kuma rage asara ga ‘yan kasuwa, wanda jinkirin yin lodi akan lokaci ke haifarwa.
Har ila yau, wannan tsarin zai rage cin hanci da rashawa a tashar, duba da cewa, yadda motoci ke zirga-zirga babu tsari, ko kuma a tauye wa wasu hakki, ko a jinkirta musu layi, yanzu wannan sabon tsarin na aiki da fasahar zamani, ya daƙile wannan badaƙalar.
Masu ruwa da tsaki a fannin, sun ce amincewa da tsarin kula da zirga-zirgar manyan motocin na dijital, ya nuna muhimmin mataki wajen dawo da doka da oda da tsari a tashar Jiragen Ruwa ta Onne, wanda hakan zai inganta saurin kwashe kayayyakin da jiragen ruwan suka kwaso, zai kuma inganta tsarin zuba jari ga harkokin safarar manyan motoci da masu dakon kaya.
Da yake tsokaci kan aiwatar da wannan tsari, Shugaban Majalisar Tuntuɓa kan Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPCC), Reshen Onne, Godwin Ololuke, ya ce, kammala shirye-shiryen tsarin kiran motoci don jigilar kayayyaki ta hanyar dijital, abun yabo ne da alfahari a tashar jiragen ruwa ta Onne.
Ololuke ya kara da cewa, ana sa ran wannan shiri zai sauƙaƙa shigar manyan motoci, rage yawan ajiye motoci a kan hanyoyin shiga tashar jiragen ruwa, da kuma inganta hasashen aiki ga masu amfani da tashar jiragen ruwa.
Wani direban babbar mota, Johnbull Igbikiowubo, ya bayyana shirin a matsayin abun da aka daɗe ana jira, kuma ya zo akan lokaci
[ad_2]
Source link