Kotu ta ɗaure boka watanni 11 a Anambra

[ad_1]



Wata Babbar Kotu da ke Awka a Jihar Anambra ta yanke wa wani boka mai suna Chigozie Nwangwu hukuncin ɗaurin watanni 11, bayan samun sa da laifukan da ake tuhumarsa da su.

Bokan, wanda aka fi sani da laƙabin “Akwa-Okuko Tiwalu Aku”, ya shahara a kafafen sada zumunta inda yake tallata kansa tare da yi wa mabiyansa ayyukan tsibbu.

A watan Fabrairun shekarar da ta gabata ne wata ƙungiyar tsaro ta yankin Agunechemba ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Jude Obiora.

An gurfanar da bokan tare da wasu mutum biyu; Onyebuchi Okocha mai inkiyar Onyeze Jesus da Ekene Igboekweze, wanda aka fi sani da Eke Hit.

Ana zargin su da haɗa baki da tsoratar da jama’a ta hanyar amfani da tsafi da dabo, lamarin da ya saɓa da dokokin tsaro na cikin gida da gwamnan jihar, Chukwuma Soludo, ya kafa.

Duk da roƙon sassauci da lauyansa, Ogwuedom Iwuobato, ya yi, kotu ta aike da shi gidan gyaran hali inda zai shafe watanni 11.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *