Trump na yi wa ƙasashe da NATO matsin lambar su taimaka masa a buɗe Mashigar Hormuz
[ad_1]
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya buƙaci ƙasashe da dama da kuma ƙungiyar tsaro ta NATO da su aike da jiragen ruwan yaƙi domin taimakawa wajen tabbatar da tsaron Mashigar Hormuz, a yayin da Iran ke ci gaba da barazanar kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa sakamakon yaƙin da take yi da ƙawancen Isra’ila da Amurka.
Trump ya ce sojojin Amurka sun “lalata gaba ɗaya” garkuwar sojojin Iran a Tsibirin Kharg, tsibirin da ke kusan kilomita 30 daga gaɓar Tekun Fasha, wanda shi ne babbar tashar fitar da ɗanyen man Iran.
Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa yana fatan ƙasashe kamar China, Faransa, Japan, Koriya ta Kudu da Birtaniya za su tura jiragen ruwa domin tabbatar da cewa Iran ba ta hana jiragen ruwa wucewa ta mashigar ba.
Rahotanni sun ce an ji fashewar abubuwa kusan 15 a Tsibin Kharg a ranar Asabar, sai dai kamfanin dillancin labaran Iran na Fars ya ruwaito cewa ba a lalata tsarin samar da man ƙasar ba.
Matsin lamba ga NATO da ƙasashen duniya
Trump ya ce yana tattaunawa da ƙasashe da dama domin taimakawa wajen buɗe Mashigar Hormuz, wadda rufewarta ta janyo tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Ya kuma yi gargaɗi cewa idan NATO ba ta taimaka wa Amurka ba, ƙungiyar za ta fuskanci “mummunar makoma”, kamar yadda ya faɗa a wata hira da jaridar Financial Times.
A halin yanzu, Japan da Australia sun bayyana cewa ba za su tura jiragen ruwan yaƙi ba, duk da cewa Japan ta ce za ta fitar da rarar man da take da shi domin rage tasirin ƙarancin man da rikicin ya haifar.
Rikicin dai na ci gaba da tayar da hankali a kasuwar makamashi ta duniya, yayin da farashin ɗanyen mai ke ci gaba da tashi sakamakon fargabar rufe Mashigar Hormuz, wadda guda ce daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai a duniya.
EU na duba yiwuwar buɗe Mashigar Hormuz
Babbar jami’ar kula da harkokin tsare-tsare na Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), Kaia Kallas ta ce ƙasashen Tarayyar Turai na shirin fara tattaunawa kan matakan da tarayyar za ta ɗauka wajen tabbatar da buɗe Mashigar Hormuz.
“Yana daga cikin muradanmu tabbatar da cewa Mashigar Hormuz ta kasance a buɗe,” in ji Kallas, gabanin taron ministocin harkokin waje na tarayyar a Brussels, kamar yadda Reuters ya ruwaito.
Wannan dai ba ya rasa nasaba da kiran da Trump ya yi wa ƙasashen na Turai da ma na ƙungiyar tsaro ta NATO da su taimaka wajen tabbatar da cewa mashigar ta kasance a buɗe.
Ofishin firaiministan Birtaniya ya sanar a ranar Lahadi cewa Mista Trump ya tattauna da Firaiminista Keir Starmer dangane da muhimmancin buɗe mashigar ta Hormuz domin daƙile yanayin da sufurin makamashi ke fuskanta a duniya.
Barazanar Iran ga Netanyahu
A gefe guda kuma, rundunar dakarun juyin-juya hali ta Iran (IRGC) sun yi barazanar “farauta da kashe” Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ya shiga mako na uku.
A cikin wani saƙo da suka wallafa a shafin su na Sepah News, rundunar ta ce idan Netanyahu na raye, za su ci gaba da farautarsa domin ya fuskanci sakamakon abin da suka kira aikata laifuka.
A daidai wannan lokaci Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya a yankin Tekun Fasha, inda aka ji ƙarar fashe-fashe a Manama, babban birnin Bahrain.
Haka kuma Saudiyya ta ce ta lalata jiragen yaƙi marasa matuƙa guda 10 da suka nufi Riyadh, sai dai Iran ta musanta hannu a harin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link