AFCON 2026: Nijeriya Ta Fara Da Ƙafar Dama
[ad_1]
Daga Rabilu Sanusi Bena
Tawagar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles) ta Nijeriya ta doke abokiyar karawarta ta kasar Tanzania da ci 2-1 a wasan farko da suka buga na gasar kasashen nahiyar Afirika a filin wasa na Fes dake birnin Fes.
Semi Ajayi ne ya fara zura kwallo a ragar Tanzania minti 36 da fara wasan bayan Alex Iwobi ya cillo masa kwallon ta sama, bayan dawowa hutun rabin lokaci ne Tanzania ta farke kwallonta a minti na 50 daidai ta hannun Mombwa.
Minti 2 da jefa kwallon Ademola Lookman ya dawowa Nijeriya da ruhinta bayan ya daki kwallon da mai tsaron raga Foba Masudi ya kasa cimmawa.
Yanzu Nijeriya ta dare saman teburin C bayan da samu maki uku da kwallo daya, sauran kasashen dake cikin rukunin na C Uganda da Tunisiya zasu hadu da junansu a Daren Yau Talata.
[ad_2]
Source link