Yilwatda ya ayyana Fubara a matsayin jagoran APC a Ribas

[ad_1]



Shugaban Jam’iyyar APC na ƙsaa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana Gwamna Sim Fubara a matsayin jagoran jam’iyyar a Jihar Ribas.

Yilwatda ya kuma ce zai mara wa Fubara baya a wa’adi na biyu idan ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Da yake magana a shirin Hard Copy na Channels Television, Yilwatda ya ce: “Gwamna Fubara shi ne jagoran APC a Ribas, amma dole ne ya yi aiki tare da sauran shugabannin jam’iyyar a jihar.”

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sake tashin rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan matsayin jagoranci a jihar.

A watan Disamba da ya gabata, bayan sauya shekarsa zuwa APC, Fubara ya ayyana kansa a matsayin jagoran jam’iyyar a Ribas, bayan da aka ba shi katin zama ɗan jam’iyya mai lamba 001.

Sai dai Wike ya yi watsi da wannan iƙirarin, inda ya ce shi ne ke da ikon sarrafa tsarin siyasa a jihar, ganin cewa APC da PDP sun haɗa kai wajen mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen 2027.

Yilwatda ya ce: “Ba ni da ikon zaɓar wanda zan goyi baya a zaɓen fidda gwani na jihar. Idan Fubara ya fito a matsayin ɗan takarar APC, zan goyi bayansa. Idan kuma bai yi nasara ba, zan ji tausayinsa, sannan in mara wa wanda ya lashe zaɓen baya.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *