Abin da ya hana ni tarbar Sarki Sanusi a Bikin Hawan Nasarawa — Gwamnan Kano
[ad_1]
A kwanakin nan ana ci gaba da yaɗa jita-jitar cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da Sarki Muhammadu Sanusi II ta hanyar ƙin halartar Bikin Hawan Nasarawa da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.
Sai dai Gwamnatin Kano ta tari hanzarin masu yaɗa wannan jita-jitar da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta, inda ta bayyana dalilin rashin halartar gwamnan a yayin bikin da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano ranar Lahadi.
A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin, ya jaddada cewa babu wani abu na raini ko wulaƙanci da aka yi wa Sarkin Kano.
Gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya tsagwaronta, mai cike da ruɗani kuma mara tushe, wadda ta ce an ƙirƙiro labarin ne da nufin yaudarar jama’a da kuma haddasa saɓani a tsakanin al’umma.
A cewar sanarwar, rashin halartar Gwamna Yusuf a taron Hawan Nasarawa ta samo asali ne sakamakon bikin ya ci karo da wasu abubuwa da suka taso musamman taron gwamnonin Najeriya wanda aka shirya gudanarwa a Legas wanda ake buƙatar halartarsa.
Duk da rashin halartar sa, an bayyana cewa Gwamna Yusuf ya bi dukkan ƙa’idoji ta hanyar sanar da Sarkin na Kano tun da wuri. Haka kuma ya ba da umarni ga manyan jami’an gwamnati su wakilce shi.
Daga cikin waɗanda suka wakilci shi akwai Kakakin Majalisar Dokokin Kano da sauran manyan jami’an gwamnati, waɗanda suka karɓi Sarkin na Kano a madadin gwamnan a Gidan Gwamnati.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnan ya halarci wasu muhimman bukukuwan Sallah. Ya yi sallar Idi da Sarkin Kano ya jagoranta, sannan ya halarci Hawan Daushe da aka gudanar a masarautar Gaya.
Bugu da ƙari, sanarwar ta ce gwamnan ya karɓi sarakunan Rano da Karaye da kuma Gaya da kansa, wanda ke nuna ƙoƙarinsa na ƙarfafa alaƙa da girmama sarakunan gargajiya.
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada cewa babu wata matsala ko rashin fahimta tsakanin gwamnati da Masarautar Kano.
Ta ce dangantakarsu na nan daram bisa mutunta juna da kuma haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link