Sojoji Sun Kama Mai Bai Wa ‘Yan Ta’adda Bayanai A Adamawa

[ad_1]

Sojojin Operation HADIN KAI tare da haɗin gwiwar mafarauta da kuma ‘yan banga sun kama wani mutum da ake zargi da bai wa ‘yan Boko Haram da ISWAP bayanai a yankin Gombi.

An kama shi ne a ranar 23 ga watan Maris bayan da jami’an tsaro suka samu sahihan bayanai kan ‘yan ta’adda a yankin da ke ƙarƙashin kulawar rundunar Bataliya ta 232.

  • An Kashe Ƴan Ta’adda 500 A Hare-haren Ngoshe Da Fatori – Zulum
  • Yaƙin Amurka Da Iran: Muna Shirin Ƙulla Yarjejeniya – Trump

Wanda ake zargin, Abdullahi Umar mai shekaru 25, ɗan asalin Gwoza ne.

Bincike ya nuna cewa an ɗora masa alhakin lura da hanyoyi da wuraren sojoji domin taimaka wa ‘yan ta’adda su gano wuraren da za su kai hari.

Haka kuma, ya amsa cewa yana da hannu a wani hari da aka kai wa sojoji a Ngoshe, lamarin da ya ƙara nuna alaƙarsa da ayyukan ta’addanci.

A halin yanzu yana hannun sojoji yayin da ake ci gaba da bincike domin gano cikakkiyar rawar da ya taka da kuma wasu da ka iya kasancewa tare da shi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *